Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuÉ—in 2023, hatsarin mota ya kashe mutum 18 Bauchi

 Wannan maƙalar ta duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi.


Shugaban ya Sanya Hannu Kan kasafin kuɗin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan buki da aka yi a ranar Talata a fadarsa da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne kwana shida bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin.

Kasafin ya ƙunshi naira tiriliyan 6.6 na biyan bashin da ake bin ƙasar, da naira tiriliyan 8.3 na ayyukan yau da kullum, sai kuma naira tirilayn 5.9 na manyan ayyuka.

Wasu ɓangarorin da suka samu kaso mafi tsoka su ne ma’aikatar tsaro wadda aka ware wa naira biliyan 285, da ma’aikatar lafiya mai naira biliyan 134.9, da ma’aikatar makamashi mai naira biliyan 195.5, sai ma’aikatar ilimi wadda ke da naira biliyan 153.7.

A lokacin sanya hannu kan kasafin kuɗin, shugaba Buhari ya ce ya lura da cewa majalisar dokoki ta sanya wasu ƙarin ayyuka a cikin kasafin, inda ya ce ya sanya hannu ne domin samun damar fara aiwatar da kasafin cikin hanzari.

Sai dai ya umurci ministar kuɗi da ta tattauna da majalisar domin duba sauye-sauyen da majalisar ta yi wa kasafin da shugaban ya gabatar mata tun da farko.

Shugaba Buhari ya kuma buƙaci majalisar da ta sake duba buƙatar da ya gabatar mata na amincewa da basukan da gwamnati ta karɓa daga babban bankin ƙasar (CBN).

Hatsarin mota ya ƙona mutum 18 ƙurmus a Jihar Bauchi


Shugabar Ofishin Kula da Basuka a Najeriya Patience Oniha ta ce duk gwamnatin da za ta gaji ta Shugaba Muhammadu Buhari a ƙarshen watan Mayu za ta tarar da bashin da ya kai kusan naira tiriliyan 77.

Ta bayyana haka ne ranar Laraba yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da kasafin kuɗin ƙasar na 2023, wanda gwamnatin za ta cike giɓinsa ta hanyar ciyo bashi.

Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta ce za a samu kashi 22 cikin 100 na kuɗin shigar da aka yi hasashe ta hanyar cinikin man fetur, yayin da za a samu kashi 77 daga wasu harkokin daban.

Don cike giɓin, ministar ta ce sai an karɓo bashin naira tiriliyan 7.04 a cikin ƙasar da kuma tiriliyan 1.76 daga ƙasashen waje. Haka nan za a karɓo tiriliyan 1.77 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma sayar da kadarorin gwamnati da za su samar da naira biliyan 206.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan kasafin kuɗin na 2023 kan sama da naira tiriliyan 20, wanda ke da giɓin tiriliyan 11.



This post first appeared on Duniyar Net, please read the originial post: here

Share the post

Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuÉ—in 2023, hatsarin mota ya kashe mutum 18 Bauchi

×

Subscribe to Duniyar Net

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×