Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

An Cafke Matasa 2 Kan Kashe Abokinsu Har Lahira Kan Shinkafa ‘Yar Hausa A Jihar Legas

Wasu Matasa Sun Kashe  Abokinsu Mai Suna Segun Zusu, Kan Buhun Shinkafa 36, Bayan Sun ‘dirkaka Masa ‘dan Banzan Duka, Kana  Suka Siyar Da Shinkafar Don Samun Kudi.


Lamarin Ya Faru Ne A Kogin Novo, Dake Jihar Legas,  Tsagerun Matasan Sun Hallaka Abokinsu Ne A Jirgin Ruwa Bayan Sun Lallasa Shi Da Duka ,  Daga Karshe  Suka Jefar Da Shi A Kogin.




Bayan Sun Kashe Abokinsu, Sun Kwashe Shinkafarsa Zuwa Wani Gari Sannan Suka Siyar Da Ita, Kana Suka Raba Kudin Shinkafar Tsakaninsu Da Wani Direban Tasi.



Matasan Da Suka Yi Aika-aikar Sune, Rajay Zannu Da Noah Tovohome, Sai Dai Wata Kotu A Birnin Legas Ta Umarci Ci Da Garkame Matasan Gidan Gyara Hali Na Kirikiri Har Zuwa Lokacin Da Bangaren DPP  Zai Yanke Hukunci A Kansu.




This post first appeared on Daily News, please read the originial post: here

Share the post

An Cafke Matasa 2 Kan Kashe Abokinsu Har Lahira Kan Shinkafa ‘Yar Hausa A Jihar Legas

×

Subscribe to Daily News

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×