Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

Shiga soja aiki ne na kare ƙasa ba aikin samun kuɗi ba


 Babban Hafsan Sojin ƙasa na Najejriya Laftanar Janar Forouk Yahaya ya ce bai kamata a ɗauki aikin soji a matsayin sana'ar samun kuɗi ba kamar sauran sana'o'i.

Janar Yahaya ya bayyana haka ne bayan da ya ziyarci sansanin tantance sabbin sojojin da rundunar sojin ƙasar za ta ɗauka aiki a cibiyar tantance lafiya da cancantar soji da ke dajin Falgore a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Yayin da yake bayyana matsayarsa, babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar ya ce saɓanin sauran sana'o'i, shi aikin soji amsa kira ne domin tsaron ƙasa, dan haka ake buƙatar 'yan ƙasar masu cikakkiyar lafiyar gaɓɓai da ƙwaƙwale tare da fikira.

Ya ƙara da cewa shiga aikin soji ba sana'a ce ta samun kuɗi ba, a maimakon haka aiki ne na hidimta wa ƙasa, dan haka yake buƙatar sadaukarwa, da jajircewa da kuma juriya, domin kuwa ba aiki ne na gama-garin mutane ba.

Babban hafsan sojin ƙasan ya shawarci matasan da ake tantancewar da su maida hankali domin kuwa waɗanda suka nuna ƙwazo ne kaɗai za su samu nasarar tsallake matakin tantancewar.



This post first appeared on Duniyar Net, please read the originial post: here

Share the post

Shiga soja aiki ne na kare ƙasa ba aikin samun kuɗi ba

×

Subscribe to Duniyar Net

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×