Wata mummunar ambaliyar ruwan da ba a taba ganin irinta ba a Cikin shekara fiye da 50, da ta shanye gefen Kogin Nilu a bara, ta sa dubban 'yan Sudan ta Kudu kaura zuwa wasu tsofaffin barikokin soji da ke kan tudu.
Inda ta shafe tsawon kwana guda tana iyo a cikin kogin, tana jan buhun da yaran ke ciki har ta isa garin Bentiu.
A yanzu iyalin na zaman gudun hijira a can, amma ba su da abinci sai suke zuwa kogin suna shuka wani abin da ake kira "yell", abin da suke ci kenan domin su rayu.
Sansanin 'yan gudun hijirar da ke Bentiu na dauke da mutane fiye da 112,000 kuma sansanin na sama wani tudun da aka gina don kare ambaliyan ruwa.
Jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Joshua Kanyara, ya ce wurin a bushe yake saboda ginin da kungiyoyin agaji suka yi ya kai tsawon mita 2.5 (kafa 8 da inci biyu).
Gatkuoth Makal Kuir (wanda ke hoto na sama) yana da shekara 19 lokacin da ya isa sansanin 'yan gudun hijirar a shekarar 2014, bayan ya kwashe kwana hudu yana tafiya da kafa, domin tserewa dakarun gwamnati da suka ce kauyensu na boye abokan gaba.
A yanzu shekarsa 27, kuma yana son komawa gida, amma baya jin zai iya daukar nauyin matarsa da dansa idan sun koma saboda ambaliya.
Yana wuni wajen neman itace, inda yakan yi tafiya mai nisan gaske, a don haka rashin tsaro na damunsa, musamman ma saboda rahotannin da suka samu na cewa dakaru sun kwashe wasu matasa 30, inda suka tilasta musu shiga soji kuma aka kashe su a fagen daga.Nyawoura Dak Top (wadda ke hoto na sama) ta yi zaman gudun hijira a wani sansani da ke kasar Kenya,ta dawo wannan sansanin a bara domin neman mahaifiyarta.
An shaida mata cewa ta rasu a lokacin da aka fara yakin, amma lokacin da ta ji cewa mai yiwuwa tana Bentiu, sai ta zo nemanta.
Sun shiga cikin farin cikin da baya misaltuwa a lokacin da suka hadu, kuma tun daga sannan suke zaune tare.
Sai dai Nyawoura tana jinta a takure, a wannan sansanin saboda ci gaba da fuskantar ambaliyan ruwa. Tana so ta yi karatu, amma tana tsoron 'yan uwanta za su iya yi mata auren dole.