Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

An kai wa offisoshinmu hari sau 50 cikin shekara uku - Inec kenan

A cewar bayanan da National Electoral Commission (Inec) ta fitar ranar Juma'a, hare-haren sun afku a jiha 15 jimilla, waɗanda suka haɗa da Imo (11), Osun (7), da Enugu (5), da Akwa Ibom (5), da Ebonyi (4), da Cross River (4), da kuma Abia (4).

Sauran su ne: Anambra (2), Taraba (2), Kaduna (1), Borno (1), Bayelsa (1), Ondo (1), Lagos (1), Ogun (1).

Shekarar 2020 ce shekarar da aka fi samun hare-haren inda aka kai sau 22, sai 2021 mai 12, da kuma 2019 da 2022 da A farkon makon nan wasu 'yan bindiga suka kai hari kan hedikwatar Inec ɗin da ke Jihar Imo, wanda shi ne hari na uku irinsa da aka kai cikin kwana 12 a jihar.

An fi samun hare-haren a jihohin kudu maso gabas, inda ƙabilar Igbo suka fi rinjaye, waɗanda hukumomi ke zargin mayaƙan ESN na ƙungiyar Ipob da ke neman kafa ƙasar Biafra da kaiwa.

Hukumar zaɓen ta ce tana da niyyar sauya wa wasu daga cikin matsugunanta mazauni a wuraren da take fama da irin waɗannan hare-hare.

A farkon nan ne Inec ta fara raba katin jefa ƙuri'a a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi ga mutum miliyan 93 da ta ce su ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙasar.

A ranar 25 ga watan Fabarairun 2023 ake sa ran fara kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen da 'yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da 'yan majalisar tarayya da na jihohi.

Yadda aka kai hare-haren a jihohi



An kai hari sau huɗu a Jihar Akwa Ibom a 2019, biyu a Imo, da kuma ɗai-ɗai a jihohin Bayelsa da Osun.

A 2020, an kai hari biyar a Osun, huɗu a Cross River, huɗu a Imo, uku a Abiya, biyu a Taraba, ɗaya Anambra, ɗaya a Legas, ɗaya a Ondo, sai kuma ɗaya a Borno.

A 2021 kuma, hari uku aka samu a Ebonyi, uku a Enugu, biyu a Imo, ɗaya a Anambra, ɗaya a Abiya, ɗaya a Kaduna, da kuma ɗaya Akwa Ibom.

Bugu da ƙari, a 2022, an samu tashin hankali sau uku a Imo, biyu a Enugu, da kuma ɗai-ɗai a jihohin Ebonyi da Ogun da Osun.

Inec ta ce rahoton bai ƙunshi ƙonewar da ofisoshin suka yi ba sakamakon gobara da sauran haɗurra kamar ruwan sama da iska.                            



This post first appeared on Duniyar Net, please read the originial post: here

Share the post

An kai wa offisoshinmu hari sau 50 cikin shekara uku - Inec kenan

×

Subscribe to Duniyar Net

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×