Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 50

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️


*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️



°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/w0hnTVda2wQ 

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-50-hausa.html


*^ Part 50 ^*



Saratu ta kalli Murja hade da cewa, "Anya Jamsy lafiya take kuwa?". Murja ta ce, "To gata nan dai". Da gudu ta fada falon ta nufi Hajiya Lami, tana fadin, "Aljana-aljana". Ai kuwa Hajiya Lami ta tashi tayi hanyar saman bene a guje, Mama Dije ma tashi tayi cikin sauri ta rufa musu baya tana waigen kofar shigowa falon, amma bata ga komai ba. "Ke Jamsy tsaya ki mana bayani, sai cewa kike aljana, aljana a ina take aljanar?". Basu Jamsy bata ce kala ba haka zalika basu daina gudu ba sai da suka shiga dakin Hajiya Lami. Mama Dije ta karasa da kyar suka bude mata, don da farko sun zata aljanar ce. "Ke tun dazun nake tambayarki a ina kika ga aljanar?". Jamsy tana haki ta ce, "Wallahi yanzun nan na ganta a cikin bangaren baki wajen su Saratu, kuma har magana tayi mun". Hajiya Lami tace, "Aljana kuma da rana anya ba tsorata kawai kikayi ba? Muje bangaren nasu mu gani". Hajiya Lami ta fada tana kallon Jamsy, "Da wa za'aje?" A cewar Jamsy "Dake za'aje mana ba ke kika ga aljanar ba". "Tabb wallahi ba zanje ba ni kam". Mama Dije ta bude kofa a hankali ta leko waje, ta duba ko ina bata ga ko bera ba, ta juya cikin dakin tayi tsaki hade da cewa, "Ke rabu da wannan shirmammiyar yarinyar watakila kawai tsorata tayi". 


Hajiya Lami ta ce, "Ni fa a lamarin gidan nan yanzu ko me akace an gani ba zan musa ba, don Allah Mama sake kiran Sailuba din, in so samu ne ta nemo mana mai cire aljannu ma a taimaka azo a cire mana aljanar da ke kokarin addabarmu a cikin gidan nan". Mama Dije na kokarin danna kira kenan sai ga kiran Sailuba ya fado wayar, ta dauka hade da karawa a kunne, "Haba Sailuba wannan wane irin abu ne, tun dazun muke kiran ki a waya amma kin ki dauka". Daga can ta ce, "Don Allah Hajiya Dije kiyi hakuri, wallahi wayar ce na saka a sailat yake ko salon ban kula ba, shiyasa ba'a jin kara sai ko an kira ni, yanzu haka daukko wayar nayi ina dubawa sai na ga kiranki, so nake yara su zo in basu su cire min abinda na sa". Cikin kosawa Mama Dije ta ce, "Kinga ba wannan dogon turancin nake bukata ba, yanzu dai ki saurareni da kyau, akwai matsala a gidan nan namu". Sailuba ta ce, "Subhanallahi! Matsala kuma wace iri? Kar dai wannan mayyar yarinyar ce Murja?". Mama Dije ta ce, "Ta Murja yanzu ai mai sauki ne tunda Kare Dangi Ya bamu mafita, wallahi muna zargin akwai aljannu ne a cikin gidan nan, kuma bibiyarmu suke daya bayan daya, idan baki manta ba na taba baki labarin an tsorata ni kwana biyu da suka wuce, to yanzu haka ga Jamsy nan tun tsakar dare aljannu suke tsoratata".  


Sailuba ta ce, "Aljannu kuma? To babbar magana, yanzu ya za'ayi?". Mama Dije ta ce, "Ai ke kika san yanda ya dace ayi, mu dai burinmu duk yadda za'ayi a zo a cire aljannun gidan nan, kama daga kan malamai bokaye ke ko yan bori ne a kawosu su zo in dai zasu iya cire aljannun dake damunmu a gidan". Jamsy tayi wuff ta ce, "Wallahi kar a daukko malamai, domin bisa dukkan alamu aljanar bata tsoron karatu, domin ita da kanta jiya ta sa nayi mata karatun alqurani". Sailuba ta ce, "Ku kwantar da hankalinku Hajiya Dije, ina nan tafe ba da dadewa ba kuma zan kawo wadanda zasu cire aljannun ko sun kai su dari ne". Hajiya Dije tayi dariya hade da cewa, "Wallahi shiyasa nake kaunarki Sailuba, domin duk wata matsala kinsan yadda za'a maganceta". Daki suka ji ana kwankwasawa, nan take suka ja da baya suna zarewa juna idanu. Jamsy kuwa tuni tayi wani irin tsalle, ta haura bayan gadon Hajiya Lami tana leken kofa. "Waye? Waye?". Hajiya Lami ta fada tana nufar baki n kofar a hankali. Shiru suka ji ba'ayi magana ba, amma kuma ana cigaba da buga kofar, Mama Dije kamar zatayi kuka ta fara magana, "Mu dai mun shiga uku, wannan wace irin rayuwa ce, ace da rana ma aljannu ba zasu bar mutum ya huta ba?". Ji sukayi an kyalkyale da dariya daga bakin kofa, nan take dukkan su suka kara tsorata.


"Wallahi dama na fada na ce ku kuke tsorata kanku da kanku, sai ku ce wai aljana ce, to yanzu dai ga shaida". Khalil dake bakin kofa daga waje ne ya fadi haka, Jamsy ta ce, "Mom kamar muryar Yaya Khalil nake ji". Hajiya Lami ta ce, "Nima na ji kamar muryarsa ce". Daga waje yana dariya yace, "Mom wallahi nine". A tsorace ta je ta bude kofar a hankali, dogon tsaki tayi ganin Khalil a tsaye yana mata dariya. Mama Dije ta ce, "Dan banzan yaro duk kasa mun tsorata". "To ai dama na fada ba wata aljana kune kuke tsorata kanku". Ya dubi Hajiya Lami hade da cewa, "Mom zuwa nayi ki dan sa mun kudi wallahi account dina yayi low kuma yau ma muna da wani party, bana so naje wajen inji kunya". Harara ta wurga masa hade da cewa, "Ina kudin da Dadynku ya saka maka kwana biyu da suka wuce?". "Haba Mom dubu dari ne fa kacal ai har ya kare". Jamsy ce ta fito daga inda take, "Mom wallahi idan kika sa mai kudi nima sai an saka min". Ya kalleta cikin daure fuska hade da cewa, "Ni sa'an wasanki ne? Zan babballaki a wajen nan". Kun ga ya isa kowa zan saka masa, ni yanzu bana son hayaniya ku ma fita ku bamu waje da abinda yake damunmu". Hajiya Lami ta fada tana nuna musu kofar fita. 


Wajejen karfe biyu, zaune suke a inuwar bishiya da ke dayan bangaren gidan suna shan rake, suka ga napep ya faka, yar dattijuwar mace ta fito tare da wani katon gardi, yana rataye da jakar fata a wuyansa, sannan hannu da kafofunsa da wuyansa cike suke da layoyi. Ganin sun nufi gidan suna shirin shiga, Hamza ya ce, "Kai! Kai! Ina zaku je?". Yayi saurin tashi ya nufi wajen Sunusi ma ya bishi baya. "Malamai ina zaku je ne haka?". Sailuba ta kalli Sunusi dake tambayarsu ta washe baki hade da cewa, "Mai gadi baka ganeni bane? Zuwa yanzu ai ya ci ace ka wayi fuskata don gidan nan gidan zuwana ne". Hamza ya bata rai hade da cewa, "Hajiya ba fa batun mun sanki ko bamu sanki bane, mu ba'a sanar damu zuwanki ba, bacin haka gashi kin zo da wani gardi mai zubin yan bori. Juyawa tayi ta kalleshi hade da cewa, "Kai yaro ka iya bakinka, ba'a ma Naziru Mai Aljannu wargi, kuma bakon Hajiya Lami ce ina shawartarku da ku bude mana gida mu shiga kafin ran Naziru ya baci in na fadawa hajiya duk sai ranku ya baci kuma, don bakonta ne na musamman". Sunusi ya kyalkyale da dariya hade da fadin, "Bako na musamman ko dai dan maula na musaman? Wannan ai ya fi kama da dan maula, kuma ita Hajiyar ce da kanta ta ce kar mu sake barin yan maula su shigar mata gida". 


"Kai yaro ka iya bakinka, idan ka bata min rai zan sa aljannu su batar da kai daga doron kasa". Katon mutumin ne ya fadi haka yana zarewa su Sunusi ido. Hamza yana dariya ya ce, "To ai kai wannan kai kanka kama da aljannun kake, karyar banza, kira aljannun mun gani". Jikin mutumin suka ga ya fara karkarwa nan take ya runtse ido ya fara gwalgwalontu, Sailuba na ganin haka ta shiga fadin, "Ayi hakuri Naziru mai aljannu yara ne, basu sanka bane, ayi hakuri". "Barini da su marar kunyar yara, yau zan nuna musu cewa mu ba'a mana iskanci". Dai-dai lokacin Mubarak driver ya karaso wajen yana tambayar Sunusi abinda ke faruwa. Sunusi yana cikin yi masa bayani kenan, ba zato ba tsammani suka ga kan Naziru mai aljannu ya fara hayaki. Baya sukayi a dan tsorace suna kallonshi, Sailuba ta ce, "Kuyi sauri ku bashi hakuri ya fusata sosai in ba so kuke yanzu ya sa aljannu su hallaka ku ba". Sunusi ya ce, "Duk karya ne rufa ido ne, in ya isa ya sa aljannun su zo nan". Ko da jin haka nan take Naziru mai aljannu ya cigaba da karanta gwalgwalantunsa yana girgiza kai kamar wani mai hauka sabon kamu. Ba jimawa kuwa suka ga kanshi ya fara ci da wuta. Da ganin haka Sailuba ta kara rikicewa, cikin gaggawa ta kira Mama Dije a waya ta na fadin suyi sauri su fito su ba Naziru mai aljannu hakuri kar yasa aljannu su kashe masu gadi.


Da gudu-gudu sauri-sauri suka kara so bakin kofa. Mai gadi ya bude kofan daga waje, Hajiya Lami Mama Dije da Jamsy su kansu ba karamin mamaki abin ya basu ba, ganin mutum a tsaye ga wuta na ci a kansa. "Boka yi hakuri karka kira aljannun nan, yara ne basu da kunya amma zanyi maganinsu, mu da muka sa a kirawo ka domin fidda aljannu ai bai dace ka sake kirayo wasu ba". Hajiya Lami ce ke fadar haka, Naziru mai aljannu ya runtse ido hade da daina Gwalangwalontun yaren da yake, wutar dake ci a kanshi ma ta daina ci ya dubi Hajiya Lami da jajayen idanunsa ya ce, "Keee! Ni ba boka bane, ni mai aljannu ne na ci uwar boka ta'adi. Ba don kin bani hakuri yanzu ba da na nunawa yaran nan karshensu". Mama Dije ta ce, "Yi hakuri mai aljannu, ai gwara da baka kira su ba, muje daga ciki mu da muke so a cire mana aljannu ai ba ma so a kara kiran wasu ba". Gaba suka shiga ya bisu a baya. Suna cikin tafiya ya kalli wani gefe a cikin gidan ya ce, "Na ganka, kaima na ganka, duk ku bar gidan na ko na ci ubanku". Su Hajiya Lami suka kalli inda ya nuna yayi magana basu ga komai ba, Sailuba ta ce, "Kai da wa kuma? Munga kamar kana magana kai kadai". Dariya ya kyalkyale da ita, tukun ya ce, "Ai da shigowa ta na ga aljannu sun kai talatin a rabe a jikin bangon can suna shan inuwa. Suna ganina shine suka fara guduwa amma akwai masu taurin kai da suka tsaya shine nake musu shaida yadda zan ci ubansu idan basu fita ba, kinsan aljannu akwai taurin kai". 


Hajiya Lami da Mama Dije suna jinsa suka girgiza kai, alamun gamsuwa domin tun da suka ga wuta na ci a kanshi suka tabbatar da cewa ba fa karamin mutum Sailuba ta samo musu ba, ta gabansu Murja suka wuce da shi har zuwa falo, ana shiga ya fara daga kai sama yana dube-dube, sannan ya fiddo wani gashi mai kama da bindin saniya ya fara guje-guje a falon gana dukan iska yana fadin, "Zaki ci ubanki yau, sai na hallaka ki, tunda kika shigo gidan mutane kika hanasu sukuni". Su dai suna gefe suna ta kallonsa. Bayan shigar su Hajiya Lami gida Hamza ya dubi Sunusi hade da cewa, "Kai da alamu fa wannan bokan ba makaryaci bane, ban taba ganin kan mutum yana ci da wuta ba sai yau". Mubarak ya ce, "Eh to nima fa na ga abun nashi ba sauki, kana ganin fa wuta ce ke ci a kanshi amma ko damuwa baiyi ba". Sunusi ya ce, "Duk da abin nasa akwai abun mamaki amma ni na so na ga iya gudun ruwansa, ai da an bari ya kira aljannun mu ga in da gaske yake". Hamza ya ce, "Ni dai ba ruwana wallahi, in banda su Hajiya da kwashe-kwashe ko me zai sa su kwaso irin wadannan mutanen cikin gida?". Mubarak yace, "Allah yasa dai ba dan damfara suka daukko ba"............... ...



Dare yayi


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍


This post first appeared on Allhausanovels, please read the originial post: here

Share the post

ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 50

×

Subscribe to Allhausanovels

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×