Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 31

Tags: kuma daga gwaska

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️


*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️



°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-31-hausa.html


*^ Part 31 ^*



Daya Daga cikin masu zuba kunnun ne ya ga ba zai jure ba, nan take ya cakume kwalar rigar Gwaska hade da cewa, "Kai rainin wayon naka fa ya fara yin yawa, na rantse maka da Allah duk abinda kake takama da shi a nan wajen akwai wanda ya linkaka biyu don haka ka bi sannu, aikaka barzahu a wajena ba wani kayan gabas bane. Taya mutane suna aiki tukuri ka zo kana zubarwa a kasa". Bisa mamakin wannan mutumi da yake masifa sai gani yayi Gwaska ya shaki kwalar rigarshi shima ya daga shi sama kafafunsa sun rabu da kasa, ba shi kadai ba ma hatta sauran yan ta'addan da wasunsu ke busa sigari wasu wiwi wasu kuwa na gyaran bindigunsu sai da suka tsaya suna kallon ikon Allah. Domin ko makaho ya laluba jikin Gwaska ya Kuma laluba na wannan mutumi, yasan cewa Gwaska ba sa'anshi bane domin hausawa na cewa alamar karfi tana da mai kiba. 


Shi kuwa Gwaska ko kadan baya da kiba gashi saurayi ko a shekaru wannan mutumi ya fashi balle girman jiki da kumari. "An zubar da kokon kayi abinda zakayi idan ka isa. Daga yau ni ba zan lamunci ana cin zalin bayin Allah ba, taya zamu sha koko harda kosai da abinci mai dadi su kuma a basu koko kadai, kokon ma mai shegen tsami wanda ko sugar babu, to yau dole a bawa bayin Allahn can kalar abincin da muka ci". Ganin ido ya dawo garesu gaba daya kuma ta daga mutumin da sauri Safuratu da ke suffar Gwaska ta ajiye shi kasa saboda kar suyi zargin wani abu, tana sakinshi ai kuwa shima ya saketa hade da cewa, "Bantan Ubannan kayyasa, yau wai dan ta'adda ne ke tausayin mutanen da ya sata ni Jabiru jikan Jummai tunda nake ban taba ji ba, karka rainawa mutane wayo mana idan wani sabon imani ne ya zo maka ko ka manta mutane nawa ka kashe a baya ba tare da imani ba da har yanzu zakayi korafi dan an basu abinci marar dadi. Kuma da kake maganar abincin da zamu ci shi za'a basu ko ka manta cewa jiya gaba dayanmu da yunwa muka kwana saboda abinci da ya rika zubewa tun a kan wuta wani kuma sai an sauke guguwa ta bata shi". 


Safuratu bata kula shi ba, ta kalli sauran yan ta'addan dake zare mata idanu hade da cewa, "Kuyi hakuri dan Allah ku kwaso kofunan nan muje mu fara zubawa bayin Allahn can koko, da alamu yunwa suke ji ga gajiya da sukayi jiya". Wani dan gajere ne ya kalli Safuratu hade da cewa, "Kai Gwaska bama son iskanci da rainin wayo a wajen nan, wai kai uban waye da kake tunanin zaka iya canza doka ko kuma ka bawa wani umarni a cikinmu? Mutum nawa ka taba kashewa da har kake tunanin kai tantirin dan iska ne? Tambayi maza ka sha labari mutanen da na kashe da bindigar nan". Ya daga binigar dake rike a hannunsa, "Sun fi ashirin na rantse maka da assamadu, domin ko kai kanka ba don eh yane ba, da kayi mun hauka zan aikaka garin da ba'a dawowa". Safuratu ce ta karasa wajensa yayin da yake binta da kallo tamkar abin arziki tana zuwa ta daga hannu ta wanka mai lafiyayyan mari. Nan take ya dafe kuncinsa saboda zafi da radadi da ya ji, yana daga hannun tuni fuskar har ta kunbura ta nuna alamun yatsu. 


Safuratu ta ce, "Ni ubanka ne". A fusace ya dago da jajayen idanunsa yana fadin, "Ni ka mara gwaska? Ni zaka mara? Daga kaina ba zaka kara marin wani ba". Yana fadar haka ya dana bindiga hade da saita Gwaska ji kake Faww! Tuni Gwaska ya duke kasa bisa tsautsayi bullet din da ya wuce ta saman kan Gwaska ya sami wani dogon dan ta'adda a goshi, nan take ya fadi kasa matacce. Da faruwar hakan waje ya kaure da hayaniya wasu suka nufi dan ta'adda da aka kashe wasu kuma suka rike gajeran da yake kokarin sake harbin Gwaska, suna fadin a huce Kusar Yaki ka kashe Dan Bazazzage. Yanayin hayaniyar ce tayi yawa har ta jawo hankalin sauran yan ta'addan, ciki kuwa har da shugabannin daba da ke cikin bukkoki suna baccin safe. Dodo ne ya fara karasowa wajen rike da bindigarsa a kafada ya daka musu tsawa nan take gaba daya yan ta'addan wajen sukayi shiru, Cikin karaji ya fara magana, "Wane irin hauka ne wannan tun da safe kun kama yiwa mutane hayaniya me yake faruwa ne?". Wani dan siriri ya lalabo kusa da shi hade da cewa, "A huce dai Dodon maza uban Rukayya, wallahi Kusar Yaki ne ya harbe Dan Bazazzage bisa kuskure yanzu haka dai ya buda".


Goje ne ya karaso wajen hade da fadin, "Kusar Yaki ya haka? Me ya hadaku ne kasan fa bana son irin wannan rikicin yana shiga tsakaninmu da sauran dabobin da kanmu yake hade ko? Maza kayi bayani in ba haka ba kuma yanzu ka tafi inda ya tafi". Da jin haka Kusar Yaki ya zube a kasa hade da cewa, "Tuba nake Goje gogan aiki, tsautsayi ne kawai ya hau kan Dan Bazazzage domin kowa a nan ya san abinda ya faru Gwaska nayi niyar daukewa lumfashi mai duka ne ya ceci rayuwarsa, amma nayi rantsuwa ko ba yau ba sai na zare masa lumfashi da harsashina tunda har ya iya daga hannu ya mareni, abinda ko ubana bayayi wato mari amma yau wannan yaron ya daga hannu ya sharara min mari saboda kawai nayi magana". Dodo ya kalli Safuratu hade da cewa, "Kai Gwaska me ya hadaku ne da har ka mareshi yanzu gashi yana ikirarin daukar rayuwarka? Kuma sanin kanku ne bama son a sama wata baraka ko rikici a tsakanin dabobin nan namu guda uku kama daga kan mu ubannin daba da kuma ku yaran cikin daba". Kafin Safuratu ta bude baki tuni Jabiru wanda suka fara rikicin na farko ya ce, "Oga ai dama ina niyar zuwa in kai korafin gayen nan a wajenka domin ya kirkiro wata sabuwar bidi'a da ba zata taba yuyuwa ba, da farko da ya samemu muna zuba koko wanda za'a kaiwa kajin can ya zubar da kokon baki daya sannan ya ce wai ba adalci bane mu ci abinci mai dadi su kuma wadancan kaji a basu koko mai tsami marar sugar". 


Dodo ya bata rai hade da cewa, "Kai Gwaska me kake nufi da haka?". Safuratu ta bata rai hade da cewa, "Ranka ya dade Dodo duk wannan abun da nayi nayi ne domin kanmu ba dan komai ba, sanin kanka ne jiya babu wanda ya ci abincin dare a cikinmu sanadin bala'i kala-kala da ya dinga fadawa abincin, to yau da safe ina zazagayawa a cikin wadancan bayin Allah da aka kamo sai naji wasu suna kusun-kusun din cewa wai a cikin sabbin zuwa da muka kamo jiya akwai masu kambun baka tun jiya da aka kai musu tuwo suka ji ba dadi shine suka sha alwashin in dai ba irin abincin da zamu ci za'a kai musu ba to ba zamu taba cin abinci ba a wajen nan, wai ko an girka sai ya zube ko kuma ana girkawa yaki dahuwa, shiyasa ni kuma na ga abinda ya faru jiya kamar akwai kamshin gaskiya a maganarsu, don haka gwara a dibar musu abinci a cikin irin wanda zamu ci a kai musu domin a zauna lafiya" Safuratu na gama fadin hakan taji gaba daya sun kwashe da dariya, Oga guje yace, "Wannan ai zancen banza ne, ba masu kambun baka ba ko mayu ne anki a basu abinci mai dadin". 


Dodo yace, "Ai ga kosai can naga ana ta soyawa kuma babu abinda ya sameshi don haka rabu da zancen banzan nan maza a sake daukko tsatstsamar gasarar nan a sake dama musu koko da ita, kuma kai Gwaska dole zanyi maka hukunci saboda barnar da kayi mana. Sannan a matsayina na shugaban daba ina mai bawa Goje da Zaki hakuri a bisa abinda ya faru, Dan Bazazzage dai kwana ya kare zan bawa iyalansa miliyan goma da matan shanu biyar". Da jin hakan waje ya dau shewa da ihu, nan take wasu suka dauke gawar Dan Bazazzage suka nufi daji domin binneta don ba ta maganar sitira ake ba. Safuratu kuwa murmushin mugunta tayi hade da cewa, "Dani kuke zancen". Kusan kasko biyar ne wasu dattijan mata ke suyar kosan, yayin da a dayan bangaren fiye da mace biyar na kula da girkin abincin. Wani daga cikin yan ta'adan ne ya nufi katuwar randa irin ta ruwa dake cike da koko, hannunshi rike da sugar wanda ya kusan rabin buhu.  


Ya daga sugan yana zubawa a cikin kokon kenan randar ta tsage gida biyu, nan take kokon ya watse ya malale a kasa, ihu ya kwalla domin jin zafin kokon a jikinshi nan take ya fadi kasa da sauri wasu suka zo suka janye shi duk ya kone saboda kokon da zafi. Su Oga Dodo dake zaune a kan kujeru sun jira a kai musu abin karin ba karamin mamaki sukayi na ganin randa mai kwari kamar wannan ta tsage gida biyu ba. Ana cikin hakan ne sukaji wata mata dake tuyar kosai ta kwada ihu hade da yin tsalle nan take ta hankade kosan da ya kusan cika farar roba babba irinta fenti, kaskon ma ya bare ba don ta gudu ba da mai ya konata.


Sakin baki sukayi gaba daya suna kallonta, bayan Dodo ya tambayi me take wa gudu tace wai kadangare ta ga ya fito daga cikin wutar ya nufi jikinta. Ai kuwa suka hau zaginta wai a banza tayi musu asarar kosai, Goje yasa aka debo masa kosai daga daya daga cikin robobin da ake zuba kosan, yana sawa a baki ya zubdar da shi da sauri dan ji yayi kamar kullun kosan ne ya saka a baki ba kosai ba, ga kuma wani irin daci. Ba shiri suka tashi suna taba ko wace robar kosan amma duk haka yake, su kuma masu dahuwar abincin sun dade suna gwala wuta amma da sun taba shinkafar sai suji kamar yanzu suka dorata. Abin duniya ne ya ishi yan ta'addar saboda masifar yunwa da suke ji tuni har sun fara yin laushi, ai kuwa wasu daga cikin ba shiri suka ce lalai maganar Gwaska akwai kamshin gaskiya a ciki don haka Dodo ya ce ya yarda za'a bawa mutanen da aka kawo irin abincin da suke ci. 


Bayan sake dora wani sabon abincin da akayi niyar za'a bawa kowa da kowa, sannan ne abincin ya dahu lafiya kalau kuma haka aka zubawa su Murja wannan karon duk mutum biyar kwana daya. 


Ana gama cin abincin ubannin daban da yaransu sulaje suka kirga su Murja hade da rabawa aka ba kowa nashi Murja na cikin mutanen Goje haka aka kadasu suka nufi dabar Goje, ita kuwa Safuratu tana biye da su a baya sai da ta ga ko wace daba sannan ta dawo Dabar Dodo, zuwa lokacin da ta dawo tuni masu garkuwa da mutanen sun fara bin jama'a suna karbar lambar yan uwansu ana kira hade da bukatar kudin fansa................,.....


🙄 Ko yayi kadan ni dai na gaji


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍


This post first appeared on Allhausanovels, please read the originial post: here

Share the post

ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 31

×

Subscribe to Allhausanovels

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×