Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

Shugaban mabiya addinin Hindu na Kasar Indiya ya amince da tayin da babban MALAMI Na kasar Indiya Dr Zakir Naik Yayi Masa.


 Kafiri Sadhguru shugaban Mabiya Addinin Hindu na Kasar Indiya ya amince da tayin da babban MALAMI na kasar Indiya Dr Zakir Naik yayi masa.

 Wannan mukabala ba gama gari bace, itaace ta farko a kasar India, sama da mabiya addinin Hindu miliyan goma suke bauta a wurin bautar Kafiri Sadhguru,

MUKABALA TSAKANIN MUSULUNCI DA FALSAFA


Babban Malamin Musulunci wanda ya kware a fagen mukabala da wadanda ba Musulmai ba Sheikh Dr Zakir Naikh ya amsa tayin mukabala da wani hamshakin Malamin Falsafa ( Philosophy) wanda yake tashe a duniyar Falsafa wato Sadhguru Jaggi Vasudev


An tabbatar da cewa Sheikh Dr Zakir Naikh bai taba haduwa da wata mukabala mai hatsarin gaske ba kamar wannan da ya amsa zaiyi da Sadhguru, saboda kwarewar da Sadhguru yake dashi a Philosophy har ana masa lakabi da wanda ya kirkiro ilmin Falsafa wato Karl Marx na wannan zamanin


Mukabala ce za'ayi ba da masu bin addinin nasara, yahudanci, buddah ko hindu ba, mukabala ce za'a gwabza akan Falsafa, wato fannoni da suka shafi tunanin hankali akan addini da samuwar Allah, siffofin Allah da kuma wanzuwarsa, wanda Malaman Falsafa suke rikitar da kwakwalen mutane a kai


Ba kowani Malamin addinin Musulunci masani yake iya tunkarar Malaman Falsafa a mukabala ba gaskiya sai wanda ya shirya kuma ya karantu sosai 


Ana kira ga jama'ar Musulmai su taya Sheikh Dr Zakir Naikh da addu'ah, domin zai tunkari mukabala mai girma a tarihin rayuwarsa


Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya taimaki Dr Zakir Naikh akan Sadhguru, Allah Ya kunyata Falsafa da dangoginta ya sa tattaunawar ta zama sanadin Musuluntarsu

 Fatan mu shine ALLAH ya daukaka musulunci da musulmai.🤲🏻🙏🏻



This post first appeared on Musa A Zage, please read the originial post: here

Share the post

Shugaban mabiya addinin Hindu na Kasar Indiya ya amince da tayin da babban MALAMI Na kasar Indiya Dr Zakir Naik Yayi Masa.

×

Subscribe to Musa A Zage

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×