Innalillahi, Mawaki Dauda Rarara ya gamu da hatsarin mota a yau Juma’a. Mawakin ya gamu da tsautsayin ne a kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukan jiragen sama. Hadiminsa a bangaren yada labarai, Rabi’u Garba Gaya ya ce mawakin na cikin koshin lafiya. Allah ya kiyaye na gaba. Amiiiin