Get Even More Visitors To Your Blog, Upgrade To A Business Listing >>

Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya Angwance a yau



An Daura Auren ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim dake unguwar Nassarawa anan birnin Kano, Da safiyar wannan rana ta Juma'a 6 ga watan 1 na shekara ta 2023 An Daura Auren mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Amaryarsa Hauwa'u Adamu Abdullahi Dikko.

Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari shine ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance a matsayin waliyyin Amaryar wadda ake kira da Hajiyayye.

Mahalarta taron Daurin Auren sun hada da Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano Alhaji Bello Abubakar Tuta da Dan Ruwatan Ringim da sauran mahalarta da dama.

An riga da anyi mata Baiko da mai martaba Sarkin Kano ne tun cikin shekarar da ta gabata, wanda ya kasance aka Daura Auren da safiyar wannan rana, kuma ta kasance guda daga cikin zuri'ar marigayi Malam Jamo dan'uwan marigayi Sarkin Kano na 2 a daular Sarakunan Fulani Malam Ibrahim Dabo.



This post first appeared on Asua Daily Post, please read the originial post: here

Share the post

Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya Angwance a yau

×

Subscribe to Asua Daily Post

Get updates delivered right to your inbox!

Thank you for your subscription

×