“Na shiga tunanin ina riƙe da rajistar ɗalibai ina jan layi kan sunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya, har sai da na goge sunaye 32; waɗanda duk sun mutu.” Nesreen Abu ElFadel, malamar da ke koyar da darasin Arabiya da Faransanci a Marrakesh, tana tuna yadda ta ruga zuwa ƙauyen Adaseel da ke kan tsauni …